SAKONNIN SOYAYYA GUDA 10+
MARUBUCI; Abba Muhd Dan-Hausa.
NA ‘DAYA.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke
haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga
suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da
kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.
NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki
adana sunan shi a cikin d’aya daga cikin kogunan
da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya
takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi
kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da
aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan
kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi
sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da
zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda
a koda yaushe kece abu mafi kusanci da
zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai
yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya.
NA HU’DU.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta
gaskata hakan, lokaci na shud’ewa soyayyar ki
na k’aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke
cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar
da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar
ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin
zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki
a wajena. Ina k’aunar ki.
NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa
abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe
yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne
zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za
mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har
zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin
kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin
soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare
ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin
hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni
a rayuwata.
NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin
zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin
begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona
maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe
kana yin jinyar shi.
NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai
nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin
yankewa har abada. Na san burina zai cika
matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin
burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin
matata uwar ‘ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal
ko kud’i.
NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude
soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin
kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan
kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan
na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude
mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan
zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya
yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.
NA TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin
soyayyata amma sai dai wanda zan turo da
sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana
hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari
bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo
nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun
da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da
kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata.
Ina son ki.
NA GOMA.
Abba ne zaune a kan wata farar kujerar roba
cikin wani lambu mai d’auke da korayen ciyayi da
ni’ima mai dad’i, wajen da ya zamo masa wajen
hutawar shi a dukkan lokacin da ya fita wajen
aiki bayan ya yi aikin ya gaji nanne inda ya saba
zuwa ya kirawo matar shi a waya domin jin halin
da ta ke ciki tun bayan auren su wanda hakan ba
karamin burge matar tashi yake yi ba sannan
kuma yana k’ara soyayyar shi a cikin zuciyarta.
Yauma dai kamar kullum, ya fito da wayar ta shi
daga aljihu ya shiga kiranta, kamar jira ta ke yi
dama bugu d’aya ta d’aga, bayan sallama sai
kuwa ya shiga cewa da ita
“Matata Uwar ‘ya’yana maganin kukana, Salimat
a baya kafin mu yi aure na yi tinanin cewa bayan
mun yi aure ba zan ke samun kulawa da
tarairaya tare da kalaman soyayyar nan ta ki
masu dad’i ba, na yi zaton komai zai canja kamar
yadda na ke gani a wasu gidajen auren ashe mu
ba haka abun ya ke ba saima abun da ya ci gaba
ya kuma sauya sabon salo mai dad’i, Salimat ina
son ki, koda aiki nake yi yadda zan dawo gida na
tarar da ke kawai na ke yin tinani, kuma koda
abinci zan ci ina ci ne kawai saboda na rayu
amma ba wai dan ina jin dadin shi ba, ina son ki
sanar da ni abun da zan taho miki da shi idan
zan dawo gida ki kuma kular min da kanki har
zuwa lokacin da zan dawo kulawar ki ta dawo
hannuna.
A.M. ‘Dan-Hausa.
#HausaKawai.
KALAMAN SOYAYYA.
(Domin Samari Da ‘Yammata Da Ma’aurata)
MARUBUCI: Abba Muhd ‘Dan-Hausa.
NA SAMARI DA ‘YANMATA.
Na Maza:
KIN ZARCE SAURAN MATA.
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya
santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki
cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin
zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su
ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SINADARIN RAYUWA TA.
SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje
guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina
fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo
ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar
gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi
rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta
Lafiya.
ZAN SO KI JI.
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna
tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki
a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke
cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da
irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
KE CE MURMUSHI NA.
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun
masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko
kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai
isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba.
Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina
Son Ki.
SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye
saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da
akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na
yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk
saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin
zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin
shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na
tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a
tare har abada. Ina Son Ki!
HMM!! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki
sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani
tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi
mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni,
hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma
na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki
Huta Lafiya.
INA SON KASANCEWA A TARE DA KE HAR
ABADA.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar
ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda
na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke
muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta
bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji.
Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke
har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke
haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske
mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na
gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da
Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan
lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama
gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke
da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki,
cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya
fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da
ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya
sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare
da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin
kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar
da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma
ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba.
Na Mata:
INA SONKA MASOYI NA!
Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi
na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina
bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son
ka masoyi na!
MU KASANCE A TARE.
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na
da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo
sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu
kasance a tare har abada. Ina Son Ka!
INA FATAN MAFARKI NA YA ZAMA GASKIYA.
A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka
zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a
gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai
wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin
samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan
mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son
Ka!
MASOYI NA.
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga
futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin
kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.
KA ZAMA RUHI NA.
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka
gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka
har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne
kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na
yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina
Son Ka!
NA MA’AURATA.
Miji:
INA SON KI!
Ba zan iya musalta adadin yadda sonki yake
lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana. Ina
son ki matata. Babu wani abinci da yake yi min
dad’i a baki na matu’kar ba ke kika girka shi ba.
Ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin
abincinki mai dad’i. Ki kula min da kanki.
ZUCIYA TA NA CIKE DA KEWARKI MATA TA.
Mata ta uwar ‘ya’ya na. Na kan yi kewarki sosai
a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki
ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin
tinaninki. Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu
sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni. Ki
kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo
kulawarki ta dawo hannu na. Ina Son Ki.
BA NI DA KAMAR KI.
Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa
da juna. Amma ina son, ki san da cewa, a duk
inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da
tinaninki a matsayinki na mata ta da nake
matu’kar so da ‘kauna ba. Ina nan tafe a hanya
zuwa gare ki. Ki kasance mai tina cewa, ba ni da
kamar ki. Ina Son Ki.
Mata:
INA ALFAHARI DA SAMUNKA.
Hasken idaniya ta, annurin rai na. Miji na, uban
‘ya’ya na. Tabbas samun miji irinka shi ne abun
da mata da yawa suke fata. Na same ka hakan
ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace
sa’a a duniya. Ina fatan dawowarka gida lafiya,
miji na abun alfahari na.
KAI NE NAKE GANI NA JI SANYI A ZUCIYA TA
MIJI NA.
Ina fatan kana nan lafiya miji na? Ina nan zaune
cikin gida amma zuciya ta tana tare da kai. Kai
ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Ina nan
ina jiran dawowarka gida lafiya. Ina son ka. Ka
kula min da kanka.

Love Text Messages To Make Him/Her Smile
ReplyDelete