JAMB. TSARE TSAREN DA JAMB TAZO DASHI A BANA DA YADDA ZAKA RUBUTA
Sanin kowa ne duk wani dalibi da ke
bukatar wucewa makarantar gaba da secondary
a Nigeria, kamar University, Polytechnic, College
of Education da dai sauransu, to dole ne ya
rubuta, kuma ya ci jarawar shiga manyan
makarantun gaba da secondary (wato JAMB a
turance). A ko wace shekara, dubban daruruwan
dalibai ne ke yin rajisatar wannan jarabawar ta
JAMB domin samun damar shiga wadannan
manyan makarantun. Ga wadanda suka san
tsarin wannan rajistar, a ko wace shekara JAMB
na fara rajista ne a karshen shekara sannan
kuma su yi jarabawar a farkon shekara mai
kamawa. To amma a iya cewa abin yanzu ya
sauya, saboda har a wannan lokaci na sabuwar
shekara da muke ciki, JAMB ba su fara rajista
ba, ballantana ma su yi jarabawar. To ko mi ya
sanya hakan? TAbbas akwai dalilai da yawa,
babba daga cikin wadannan dalilai shine gyaran
tsarin yanda za’a iya yin rajistar jarabawar da
JAMB din suka bullo da shi. Duk da cewa JAMB
sun sauya fasalin yin rajista, da yawa daga cikin
mutanenmu, da ke da niyyar zauna wannan
jarabawar, basu san da wannan tsarin da JAMB
suka bullo da shi ba.
Sabanin yanda aka sani a baya, idan
JAMB ta fara Registration, to mutum zaya sayi
“ Scratch Card ” ne kawai ya nufi “ Café ” domin a
yi masa rajista. To a wannan lokaci ba haka abin
yake ba. A sabon tsarin da JAMB suka bullo da
shi shine, DOLE NE DALIBI YAYI RAJISTA DA
WEBSITE DINSU, WATO YAYI CREATING
ACCOUTING DINSA A SAMAN WEBSITE DIN
NASU, KAFIN YA IYA YIN RAJISTAR
JARABAWAR JAMB DIN.
Mi wannan tsarin yake nufi?
Wannan tsarin yana nufin kafin JAMB su
fara yin rajistar jarawar, dole ne dalibi ya je a
website dinsu ( www.jamb.org.ng ) ya bude
account da su. Bayan ka bude wannan account
naka, zasu baka wasu lambobi na musamman
wadanda dole sai da su ne zaka iya yin rajistar
wannan jarabawar ta JAMB idan an fara.
Yaya wannan tsari yake?
Shi wannan tsarin abin da yasa JAMB
suka bullo da shi shine, domin su saukaka yanda
dalibai zasu iya samun duk wasu bayanai
dangane da JAMB din a saukake, da kuma kare
dalibai daga ‘yan dambfara wadanda ke damfarar
dalibai.
Ya ake bude wannan account?
Domin bude wannan account, sai ka bi
wadannan matakan kamar haka:
1. Ka shiga website din JAMB a
www.jamb.org.ng
2. Bayan ka shiga sai duba daga gefe akwai inda
ka sanya Click to log in , sai ka dannan wajen
3. Wannan zaya bude maka wani shafi inda zaka
iya yin log in, to amma tun da baka da account,
sai ka duba daga kasa inda aka sanya Create
account , sai ka shiga nan
4. Wannan zaya bude maka wani shafi inda zaka
sanya bayananka (amma a sani dole ne mutum
yayi amfani da email dinsa wanda yake amfani
da shi). Bayan ka kammala sanya bayanan naka,
sai ka danna inda aka sanya “ Verify e-mail”
5. Daga nan zasu tura maka sako a e-mail din da
ka bayar. Wannan sakon e-mail da zasu tura
maka yana dauke da wani link wanda zaka
danna domin yin “ Verfying ” ko kuma
“ Confriming ” din account dinka, wato zaka
tabbatar da sahihancin wannan e-mail din da ka
bayar. Baya ga wannan link din kuma, akwai
wasu lambobi da zasu baka a cikin wannan
sakon e-mail da suka turo maka. Zaka ga
wadannan lambobi kamar haka:
23ae4-6ddfe-33fdde-ae359gh394 .
Wannan lamba ita zaka yi amfani da ita wajen
yin rajistar jarabawar JAMB din idan an fara, ka
tabbatar ka kwafi wannan lamba kamar yanda
take, ka kuma adana ta har zuwa wannan lokaci.
Shi kuma wannan e-mail naka da ka bayar, ta
nan ne JAMB zasu rika tuntubarka dangane da
duk wani abu da ya taso game da wannan
jarabawar.
Akwai mutane da dama da suke korafin
cewa basu iya bude wannan account ta wayarsu,
wasu kuma suna cewa basu iya biyan kudin da
ake karba a Café domin bude ma mutum wannan
account. Wannan ne yasa muka ga ya dace, a
matsayinmu na masu son kawo ci gaba a cikin
al’umma, muma mu bada gudummawarmu wajen
taimakawa wadanda ke da karamin karfi da kuma
wadanda basu da damar zuwa wajen da ake yin
wannan aiki na bude account. Wannan ne yasa
muka yi tanadi na musamman domin budewa duk
wanda ke da niyyar zauna wannan jarabawa ta
JAMB. Duk da cewa akwai wani dan abu da
mutum zaya bada, muna da tabbacin cewa,
wannan tsari shine hanya mafi sauki da mutum
zaya iya bi domin bude wannan account, sai dai
in mutum zaya iya yi da kansa idan yana da
computer.
Domin Karin bayani akan yanda zaku iya
amfana da wannan tsari namu, sai ku tuntubi
wakilanmu ta hanyar kira ko kuma ta Whatsapp a
wannan lambar 07061599050 . Da fatan zaku yi
amfani da wannan damar, ko ku bada taku
gudummawar wajen sanar da wadanda ke da
niyyar zauna wannan jarabawa a wannan
shekarar domin su ma su amfana.

Comments
Post a Comment