Ina yi wa membobin Majalisar Burin Zuciya da dukkanin masu karatun jaridar Leadership Hausa fatan alheri da fatan samun babban rabo a wannan babban rana ta Jumma’ah. Allah Ya sa yadda muka ga farkonta lafiya, Ya sa mu ga karshenta lafiya, sannan ya kara sada mu da dukkan alheran da ke cikinta, Ya kuma kare mu daga dukkan sharrin boye da na bayyane, amin. Na ci karo da wannan makalar a cikin wasu bincike-binciken da nake gudanarwa kan halayen mata, shi ne na ga yana da kyau membobinmu a wannan majalisa, musamman maza su fahimci wasu daga cikin halayen. Daga bisani, mu tattaro ra’ayoyin sauran jama’a, makaranta wannan jarida mai farin jini. A binciken nawa, na fahimci babbar matsalar da maza ke fuskanta a kan zama da mata a yau shi ne rashin fahimtar yarensu. Ma’ana Lugga ko salon da zantukansu da inda maganarsu ke fuskanta. Amma kafin nan, ba ri mu yi tsakaci kan mace da yadda take gudanar da harkokinta a zahirance. Masana harkokin mata, sun tafi a kan cewa mace t...